Hukumar kare haƙƙin dan Adam ta kasa ta kammala bincike kan
zargin da ake yi wa sojojin kasar na gudanar da wani shirin
zubar da ciki a asirce.
Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa a watan Disambar 2022 ya yi zargin cewa sojojin kasar nan sun zuɓar da cikin mata masu juna biyu 10,000 a yankin arewa maso gabashin kasar, tun daga shekarar 2013.
Rahoton ya ce dayawa daga cikin waɗannan matan an kuɓutar da su ne daga hannun masu iƙirarin jihadi da suka yi garkuwa da su tare da yi musu fyaɗe. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya tattauna da 33 daga cikin matan, inda ɗaya daga cikinsu ta zargi cewa sojojin ne suka zubar musu da ciki ba tare da izininsu ko saninsu ba.
Hukumar kare haƙƙin bil adama ta kasa NHRC ta kafa wani kwamitin da ya fara gudanar da bincike a cikin watan Fabrairun bara. Sojoji sun bukaci kwamitin da ya wanke su daga dukkan zarge- zargen da ke ƙunshe a cikin rahoton na Reuters, a wani sakon da NHRC ta wallafa a shafin X yayin da ta sanar da kammala binciken na ta.