Home Labaru Kasuwanci Zargin Ƙin Biyan Haraji: Gwamnatin Tarayya Ta Maka Kamfanin Binance A Kotu

Zargin Ƙin Biyan Haraji: Gwamnatin Tarayya Ta Maka Kamfanin Binance A Kotu

57
0

Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara kan kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Hukumar tara haraji ta kasa, FIRS ce ta sanar da matakin, Gwamnatin dai na tuhumar kamfanin na Binance da aikata laifuka huɗu da ke da alaƙa da ƙin biyan haraji.

Cikin waɗanda ake ƙarar akwai Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, dukkansu manyan shugabannin Binance da yanzu haka ke tsare a hannun hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Binance sun haɗa da zargin ƙin biyan harajin VAT kan kayayyakin more rayuwa da harajin da kamfanoni ke biya na kuɗin shigar da suke samu da ƙin biyan kuɗaɗen harajin da suka karɓa da kuma haɗa baki da abokanan hulɗarsu wajen kaucewa biyan haraji ta shafinta.

Gwamnatin tarayya tana zargin Binance da ƙin yin rajista da hukumar FIRS saboda dalilai na haraji da kuma saɓawa dokokin biyan haraji a ƙasar.

Leave a Reply