Home Labaru Jimami: Tsohon Shugaban Sudan Sadiq Al-Mahdi Ya Rasu

Jimami: Tsohon Shugaban Sudan Sadiq Al-Mahdi Ya Rasu

80
0

Fitaccen dan siyasar Sudan, kuma tsohon Fira Minista Sadiq al-Mahdi, ya mutu ne sakamakon fama da cutar Coronavirus makonni uku bayan da aka kwantar da shi a Hadaddiyar Daular Larabawa, a cewar wata sanarwa da jam’iyyarsa da kuma iyalansa suka fitar da safiyar yau Alhamis.

Marigayi Mahadi, mai shekara 84, shi ne zababben Fira Minista na karshe da aka zaba a kasar Sudan, an kuma hambarar da shi ne a shekarar 1989 a juyin mulkin soja da ya kawo tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir kan karagar mulki.

Jam’iyyar Umma, tana daya daga cikin manyan jam’iyyun adawa a lokacin Bashir, kuma Mahadi ya ci gaba da kasancewa mai fada a ji har bayan da aka hambarar da Bashir a 1989.

A watan da ya gabata, dangin al-Mahdi sun ce gwajin cutar coronavirus ya nuna cewa yana dauke da cutar, kuma an mayar da shi zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa don neman magani kwanaki kadan bayan kwantar da shi a wani karamin asibiti a Sudan.

A cikin wata sanarwa, Jam’iyyar Umma ta ce za a yi jana’izar marigayin da safiyar gobe Juma’a a garin Omdurman na Sudan.