Home Labaru Michael Flynn: Trump Ya Yafe Wa Jami’in Da Ya Kira “Tsarkakakke”

Michael Flynn: Trump Ya Yafe Wa Jami’in Da Ya Kira “Tsarkakakke”

83
0

Shugaban Amurka Donald Trump ya yafe wa tsohon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Michael Flynn.

Mista Flynn ne mutumin da ya amsa laifin shirgawa hukumar tsaro ta FBI karya dangane da zargin da ake yi masa na mu’amala da jami’an Rasha a kokarin yin kutse a zaɓen shugaban kasar na 2016 Shugaban ya kira matakin nasa a matsayin “abin alfahari”.

Mista Flynn na cikin makusantan shugaba Trump da ma’aikatar shari’a ta Amurka ta samu da laifin taimakawa hukumomin Rasha, wajen yin kutse a zaɓen Amurka na shekarar 2016 da zummar taimaka wa Trump.

A shekarar 2017 ne ya amince cewa ya yi wa hukumar FBI ƙarya dangane da hulɗa da jakadan Rasha a kan wannan manufa.

Fadar White House ta ce yafiyar za ta kawo ƙarshen tsangwamar mutumin da ta kira a matsayin “Tsarkakakke.”

Cikin wata sanarwa, fadar ta ambaci Flynn a matsayin wanda tuggun ƴan siyasa ya rutsa da shi.