Home Labaru Tsaro: Dakarun ‘Operation Fire Ball’ Sun Halaka ’Yan Boko Haram 23, Tare...

Tsaro: Dakarun ‘Operation Fire Ball’ Sun Halaka ’Yan Boko Haram 23, Tare Da Ceto Mutum 5

119
0

Sojojin rundunar ‘Operation Fire Ball’ a karkashin Lafiya Dole da ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabas, sun bayyana samun nasarar halaka yan ta’adda 23 tare da ceto mata uku da yara biyu daga mayakan, a wani taron manema labarai wanda ya gudana a garin Ngamdu da ke jihar Borno.

A jawabin mukaddashin Daraktan yada labarai a rundunar sojojin, ya fada wa manema labarai cewa wasu daga cikin yan ta’addan sun shiga komar su ne a sa’ilin da suke kokarin karbar kudin fansa daga hannun ’yan uwa wadanda su ka yi garkuwa da su.

Bugu da kari kuma ya sanar da cewa, mata biyu hadi da yara kanana guda uku an ceto su ne daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram wadanda ke azabtar dasu.

Mista Benard ya kara da cewa, zaratan sojojin rundunar sun kwace tarin makamai daga hannun yan ta’addan, wadanda suka kunshi motocin yaki hudu, bindigogin harbo jirgin sama guda biyu, da bindiga daya mai sarrafa kanta, sai bindigogin biyu kirar PKT, da karin guda takwas kirar Ak-47 hadi da sauran makamai.

A karshe Mista Onyeuko ya bukaci jama’a su bai wa sojoji Nijeriya goyon baya ta hanyar sanar dasu dangane da take-taken yan ta’adda a yankunan su, domin daukar matakin da ya dace.