Home Labaru Tsaro: Sojojin Nijeriya Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da...

Tsaro: Sojojin Nijeriya Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

115
0

Dakarun rundunar sojin Nijeriya ta Operation Hadarin Daji, sun ceto mutane 10 da ‘yan fashi su ka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.

Mai magana da yawun helkwatar tsaro ta Nijeriya Manjo Janar John Enenche ya bayyana hakan, inda ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne bayan dakarun su sun samu wani kiran gaugaawa daga kauyen Yenyewa cewa an ga ‘yan fashi su na zarya a yankin.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce da zuwan sojoji masu garkuwar su ka tsere su ka bar mutanen bayan an fara yi masu ruwan wuta. Manjo Janar John Enenche ya kara da cewa, tuni an hada mutanen da dangin su.