Home Labaru Gargadi: A Daina Furta Migayun Kalamai A Kan Tubabbun ‘Yan Boko...

Gargadi: A Daina Furta Migayun Kalamai A Kan Tubabbun ‘Yan Boko Haram – FG

37
0
NIGERIA-BOKO-HARAM-SURRENDERS

Gwamnatin tarayya, ta ja kunnen ‘yan Nijeriya a kan yadda su ke yawo da labarun karya dangane da tubabbun mayakan Boko Haram.

Ministan labarai da al’adu Lai Mohammed ya bayyana hakan, yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Washington na kasar AMurka.

Lai Mohammed, ya nuna takaicin sa a kan yadda mutane da dama ke musanta cewa asalin mayakan Boko Haram ne su ka yi mubaya’ar, sannan idan har da gaske su ne ya kamata a harbe su domin ba su cancanci yafiya daga gwamnati da ‘yan Nijeriya ba.

Ministan, ya musanta labarun bogin da jama’a ke yadawa, cewa za a horar da tubabbun ‘yan ta’addan su zama sojojin Nijeriya.

Ya ce ya kamata ‘yan Nijeriya su rika yaba wa gwamnati da sojoji bisa jajircewar su a kan ganin sun kawo karshen rashin tsaro.