Gwamna Matawalle na Jihar Zamfara, ya ce daga yanzu Gwamnatin Jihar ba za ta sake nema ko yarda ta yi sulhu da ‘yan bindiga ba, domin an sha yi masu tayi a baya su na karya alƙawari tare da saɓa yarjejeniyar da aka yi da su.
Matawalle, ya ce maimakon a yi sulhu da su, ya na kira ga jami’an tsaro su cigaba da zaƙulo su su na kashewa kawai.
Ya ce Gwamnatin sa ba za ta sake yi wa ‘yan bindiga afuwa ba, saboda an sha yi masu a baya, amma su na tada tuba.
Gwamnan, ya kuma roƙi al’ummar jihar Zamfara su ƙara juriya da haƙuri, tare da goyon bayan tsauraran matakan da jami’an tsaro ke ɗauka na zaƙulo ‘yan bindiga don a dawo da zaman lafiya a yankin.