Ministan Harkokin Ruwa Sulaiman Adamu, ya ce yankunan jihohin Tsakiyar Nijeriya ne aka fi yin bahaya a fili duk fadin Nijeriya.
Adamu bai ambaci sunayen jihohi ba, amma yankin tsakiyar Nijeriya ya kunshi jihohin Nasarawa, da Neja, da Kwara, da Benue, da Filato da kuma sassan garuruwan da ke karkashin Gundumar Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ministan, ya kuma koka da yadda ake yin bayan-gida barkatai a Nijeriya, inda ya ce daga cikin Kananan Hukumomi 774 na Nijeriya, 14 ne kadai jama’a ba su yin Ba-Haya a fili.
Adamu ya bayyana wannan abin takaicin ne, yayin da ya ke kare kasafin kudin ma’aikatar sa a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa.
A karshe ya yi kira ga gwamnatoci da ‘yan kasuwa su rika gina Makewayi a garuruwa da birane, ya na mai cewa akalla mutane miliyan 47 Nijeriya ke fama da matsalar rashin Makewayi.