Asusun Tallafa wa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ya gabatar da sakamakon binciken da ya yi a kan yadda ake fama da rashin koshi da ciyar da kananan yara abincin da ke gina jiki a Nijeriya.
A cikin rahoton dai, Jihar Kano ce ke kan gaba wajen yawan kananan yaran da ba a ciyar da su abinci yadda ya kamata.
Shugaban sashen masana ingancin abinci na UNICEF Simeon Nanama ya gabatar da sakamakon binciken, yayin wani taro da Asusun ya yi a Kano.
Nanama, ya ce UNICEF ta yi binciken ne a wasu zababbun kananan hukumomin da ke jihar, domin gano hanyoyin da za ta bi wajen dakile matsalar, inda ya ce kananan hukumomin Bichi da Sumaila ne aka fi samun yaran da ke watangaririya babu abinci sannan kuma a kyamushe.
Ya ce tabas, idan aka kwatanta adadin yawan yaran da ke fama da yunwa jihar Kano ce a kan gaba.