Home Labaru Ajali: Wani Direban Mota Ya Kashe Dan KAROTA A Kano

Ajali: Wani Direban Mota Ya Kashe Dan KAROTA A Kano

531
0

Wani ma’aikacin hukumar kula da cunkuson ababen hawa da aka fi kira ‘KAROTA’ a Kano ya riga mu gidan gaskiya, sakamakon buge shi da mota da wani direba ya yi a daidai lokacin da ya ke kokarin kama shi saboda ya ki tsayawa yayin da danja ta tsayar da masu tafiya a titin da ya ke a kai.

Lamarin dai, ya faru ne a kan titin zuwa filin jirgin sama na Kano kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Kakakin hukumar KAROTA Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya faru ne bayan direban ya tsaya a hanyar zuwa ofishin jami’an KAROTA, bayan sun kama shi da laifin karya dokar tuki.

Tsayawar da direban motar ya yi ne ya sa jami’in mai suna Tijjani Adamu ya fito daga motar su ta ma’aikata, domin ya kwance lambar motar da direban ke ciki bayan ya tsaya.

Kakakin ya kara da cewa, marigayin ya yi kokarin kwance lambar motar mutumin, lamarin da ya sa shi kuma ya zaburi motar, inda nan take ya buge jami’in tare da taka shi sannan ya gudu.