Home Labaru Jigon APC Ya Tsorata Da Iyorchia Ayu Kalubale A Matsayin Shugaban PDP

Jigon APC Ya Tsorata Da Iyorchia Ayu Kalubale A Matsayin Shugaban PDP

15
0

Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC reshen jihar Benue Kwamared Abba Yaro, ya bayyana kasancewar Sanata Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa a matsayin babban kalubale ga jam’iyyar APC.

Kwamared Abba Yaro ya bayyana haka ne, a wani taron jam’iyyar APC da ya gudana a birnin Makurdi na jihar Benue.

Ya ce babban kalubale ne ga kowace jam’iyya a ce shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya fito daga jihar Benue, ya kuma bukaci matasa su tashi tsaye domin gudanar da gagarumin aikin da ke gaban su.

Abba Yaro, ya ce dole ne su ajiye duk wani ra’ayi a gefe su yi abin da ya dace, su kuma gabatar da ‘yan takara masu inganci a zabe mai zuwa.