Home Labaru Hatsarin Mota: Rayuka 7 Sun Salwanta A Karamar Hukumar Maigatari Ta Jihar...

Hatsarin Mota: Rayuka 7 Sun Salwanta A Karamar Hukumar Maigatari Ta Jihar Jigawa

1021
0

Kimanin rayukan mutane 7 ne su ka salwanta, yayin da wani mummunan hatsarin mota ya auku a kan wata babbar hanya a kauyen Kwalande da ke karamar hukumar Maigatari ta jihar Jigawa.

Hatsarin dai ya auku ne tsakanin wasu motoci biyu kirar Peugot 206 da kuma Golf 3 kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

SP Abdu Jinjiri, Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a garin Dutse.

Hatsarin dai ya salwantar da rayukan mutane bakwai nan take, yayin da mutane 11 da su ka hada da direbobin motocin biyu su ka jikkata.

Tuni an garzaya da wadanda su ka jikkata tare da killace gawar wadanda su ka riga mu gidan gaskiya a babban asibitin garin Gumel.