Home Labarai Zamfara: CDS Irabor Ya Kalubalanci Umarnin Gwamna Ga ‘Yan Jihar Na Mallakar Makamai

Zamfara: CDS Irabor Ya Kalubalanci Umarnin Gwamna Ga ‘Yan Jihar Na Mallakar Makamai

437
0

Shugaban Hafsoshin tsaron Nijeriya Janar Lucky Irabor, ya kalubanci kiran da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi cewa mutanen jihar su mallaki bindigogi domin kare kawunan su daga hare-haren ‘yan bindiga.

Janar Lucky Irabor ya ce kiran bai dace ba, saboda akwai jami’an tsaro da sauran hukumomin tsaro a wajen domin magance matsalar.

Yayin zantawa da manema labarai a wani taron hadin gwiwa da Kwalejin Tsaro da Kwalejin Yaki ta dakarun sojin Nijeriya a Abuja, Irabor ya ce hakan ba hanyca ce mai bullewa ba, domin akwai matakan da hukumomin tsaro da rundunar soji ke dauka don magance matsalar rashin tsaro a jihar Zamfara da kewaye.

Ya ce tabbas akwai matsalolin da ya kamata ta shawo kai tare da amfani da dokokin da ke hannun sa domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro, amma Atoni-janar na tarayya ke da alhakin duba kundin tsarin mulki don ganin idan gwamnan ya na da hurumin daukar wannan.

Leave a Reply