Home Labaru Babu Wata Baraka Tsakanin Shugaba Buhari Da Osinbajo – Gwamnonin APC

Babu Wata Baraka Tsakanin Shugaba Buhari Da Osinbajo – Gwamnonin APC

271
0
Babu Wata Baraka Tsakanin Shugaba Buhari Da Osinbajo - Gwamnonin APC
Babu Wata Baraka Tsakanin Shugaba Buhari Da Osinbajo - Gwamnonin APC

Gwamnonin jam’iyyar APC, sun yi watsi da rahotannin cewa akwai baraka tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo, inda su ka bayyana lamarin a matsayin gulma da gutsuri-tsoma.

Yayin da su ke magana a wajen taron rantsar da kwamitin Gwamnonin APC a kan kafofin yada labarai da sadarwa, Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, ya ce ko a wannan makon mataimakin shugaban kasa ne ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta kasa.

Ya ce a matsayinsu na gwamnoni su na amfani ne da shaidu ba cece-kuce ba, yayin da ya bukaci ‘yan Nijeriya su cigaba da mara wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari baya.

A wani bangaren kuma, Jaridar Vanguard ta nemi gafarar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, biyo bayan kuskuren da ta yi na wallafa wani rahoto maras tabbas da ke dauke da kazafi da kuma bata suna.

Jaridar Vanguard dai ta wallafa wani rahoto da ke cewa, Osinbajo ya karbi kimanin naira biliyan 90 a hannun hukumar tattara haraji ta kasa domin yakin neman zaben shekara ta 2023.