Home Labaru Kiwon Lafiya Cutar Corona: Hukumar NCDC Ta Tsaurara Matakai A Tashoshin Nijeriya

Cutar Corona: Hukumar NCDC Ta Tsaurara Matakai A Tashoshin Nijeriya

496
0
Cutar Corona: Hukumar NCDC Ta Tsaurara Matakai A Tashoshin Nijeriya
Cutar Corona: Hukumar NCDC Ta Tsaurara Matakai A Tashoshin Nijeriya

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC, ta tsaurara matakai a tashoshin jiragen sama da ruwan Nijeriya domin yin riga-kafin kada a shigo kasar nan da kwayoyin cutar ‘CORONA VIRUS’ da ake kira ‘Murar Mashako’.

An dai dauki matakin ne, domin kauce wa fadawa cikin halin kaka-ni-ka-yi tun bayan barkewar cutar a kasar Chana, inda mutane bakwai su ka rasu sannan aka gano wasu 500 dauke da kwayoyin ta.

Rahotanni sun nuna cewa, cutar ta yadu zuwa kasashen Amurka da Korea ta Kudu da Thailand da Japan da kuma Asutralia.

Hukumar NCDC ta yi kira ga matafiya su tabbatar sun yi gwajin cutar a wuraren yin gwaji da hukumar ta kebe a tashoshin jiragen saman Nijeriya.