Home Home Jami’yyu 8 Sun Mika Wuya, Sun Yi Mubaya’a Ga Uba Sani, Zaɓaɓɓen...

Jami’yyu 8 Sun Mika Wuya, Sun Yi Mubaya’a Ga Uba Sani, Zaɓaɓɓen Gwamnan Kaduna

66
0
Zababben gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba sani, ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin jin dadin mutanen jihar Kaduna baki daya.

Zababben gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba sani, ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin jin dadin mutanen jihar Kaduna baki daya.

Sanata Uba Sani ya bayyana haka ne, lokacin da ya karbi baƙuncin ‘yan takara daga wasu jam’iyyun da su ka fafata da shi a zaɓen rabar 18 ga watan Maris a Kaduna.

‘Yan takarar dai, sun ce sun je ne domin su taya gwamna mai jiran gado murnar nasarar da ya samu tare da yi ma shi fatan alkhairi.

Da ya ke jawabi bayan ya saurare su, Sanata Uba Sani ya ce wannan ba nasarar shi kaɗai ba ce, nasara ce ta kowa da kowa har da su da su ka fafata da shi, sannan ya sha alwashin tafiya tare da kowa domin ci-gaba al’ummar jihar Kaduna.