Jam’iyyar PDP ta gudanar da tarurrukan zaben shugabannin ta a jihohin da su ka hada da Adamawa da Oyo da Kwara a karshen mako, sai dai zaben ya bar baya da kura sakamakon yadda rikici ya barke a tsakanin ‘ya’yan ta.
Duk da ya ke an gudanar da taron cikin lumana a jihohin Adamawa da Kwara, amma ba a wanye lafiya a jihar Oyo ba, inda ‘yan jagaliya su ka kaddamar da hari a kan wani jigon jam’iyyar mai suna Omolaja Alao.
Omolaja Alao dai shi ne shugaban Karamar Hukumar Arewa Maso Gabashin Ibadan, yayin da ‘yan dabar su ka kai masa hari a daidai kofar shiga filin taron.
Rahotanni sun tabbatar cewa, an soke gudanar da irin wannan taron sakamakon tashin hankalin da ya barke a dandalin Tafawa Balewa da ke tsibirin Lagos.
Ana gab da fara zaben ne dai, wani gungun ‘yan dabar siyasa ya yi dirar mikiya a kan jama’a, lamarin da ya sa tilas aka jingine zaben.














































