Home Labaru An Yanke Wa Tsohon Shugaban Lauyoyi Hukuncin Shekaru 3 A Gidan Yari

An Yanke Wa Tsohon Shugaban Lauyoyi Hukuncin Shekaru 3 A Gidan Yari

384
0
An Yanke Wa Tsohon Shugaban Lauyoyi Hukuncin Shekaru 3 A Gidan Gyari
An Yanke Wa Tsohon Shugaban Lauyoyi Hukuncin Shekaru 3 A Gidan Gyari

Babbar kotun tarayya da ke Yola, ta yanke wa tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Binanu Esthon da mai shari’a Shehu Mustapha hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari, sakamakon kama su da laifin damfara da ta yi.

Karanta Wannan: Babakere: EFCC Ta Kwakulo Motocin Alfarma 21 A Gidan Yari

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC dai ta zargi Esthon da Mustapha da laifuffuka 7 da su ka hada da damfara a shekara ta 2015.

Mai shari’a Bilkisu Aliyu ta kama su da laifin sata da damfarar Naira miliyan 67 daga ma’aikata 502 da su ka yi murabus na kamfanin Stirling Civil Engineering da ke jihar Adamawa a shekara ta 2007.

Ta ce Mustapha ya karbi kudin ma’aikatan da su ka yi murabus tare da kin biyan su hakkokin su, yayin da Esthon a matsayin sa na ma’aikacin shari’a da zai iya tursasa Mustapha ya biya su kudin su amma ya ki.

Mai shari’ar ta cigaba da cewa, a matsayin Esthon na lauyan Mustapha kuma masanin shari’a, ya dace ya tsaya wa adalci ne ta hanyar tabbatar da adalci a matsayin sa na lauya.