Home Labaru Kasuwanci USAID Ta Ware Dala Milyan 300 Domin Inganta Cinikayyar Amfanin Gona

USAID Ta Ware Dala Milyan 300 Domin Inganta Cinikayyar Amfanin Gona

304
0
Hukumar Tallafa Wa Cigaban Kasashe Masu Tasowa Ta Amurka, USAID
Hukumar Tallafa Wa Cigaban Kasashe Masu Tasowa Ta Amurka, USAID

Hukumar Tallafa Wa Ci-gaban Kasashe Masu Tasowa ta Amurka USAID, za ta zuba jarin dala milyan 300 domin inganta cinikayyar kayan gona nau’uka biyar a wasu jihohi bakwai na Nijeriya a karkashin shirin ta na Ciyar da Al’umma.

Jakadan Amurka a Nijeriya Stuart Symington ya bayyana haka a Abuja, a wajen wani taron Masu Ruwa da Tsaki na Zuba Jarin Harkokin Noma.

Shirin da hukumar USAID ta bijiro da shi dai zai zaburar da ‘yan Nijeriya su maida hankali ga harkar noma kayan gonar da za a rika cin nomriyar su wajen samun kudin shiga ta hanyar hada-hadar cinikayyar su.

Symington, ya ce shirin zai magance kasadar da masu cin bashi ko lamuni ke fuskanta a lokutan da su ka ranci kudade a bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi su ka zuba a harkokin noma.

Jakadan na Amurka ya kara da cewa, hukumar za ta janyo kanana da matsakaitan masana’antu 500 masu harkokin noma domin cin moriyar shirin.