Home Labaru A Karon Farko An Bi Umurnin IPOB Ta Zama A Gida A...

A Karon Farko An Bi Umurnin IPOB Ta Zama A Gida A Jihar Abia

5
0
NNAMDI-KANU-AND-IPOB

Manyan tituna sun zama wayam, yayin da shaguna da ma’aikatun gwamnati su ka kasance rufe a birnin Umuahia na jihar Abia, sakamakon dokar zaman gida da kungiyar ‘yan A-Waren Biafra ta IPOB ta sanya.

Idan dai ba a manta ba, a baya kungiyar ta sa irin wannan dokar ta zaman gida, wanda ya hada da rufe makarantu da kasuwanni amma ba ta yi tasiri ba.

A Litinin da ta gabata, mazauna birnin Umuahia sun ce ‘yan kungiyar sun rika yawo da bindigogi kan tituna su na hantarar mutane su shige gidajen su.

Sai dai mazauna birnin jahar sun sami kan su cikin tsaka-mai-wuya, bayan gwamnatin jihar ta yi gargadin cewa duk ma’aikacin da bai je aiki ba zai fuskanci hukunci, amma duk da haka kashi 80 cikin ba su je aiki ba a ranar Litinin din nan.