Babban Hafsan dakarun Sojin Nijeriya Janar Tukur Buratai, ya ce sojoji sun nemi hadawa da addu’o’i wajen yaki da Boko Haram ne domin a dakile yadda ‘yan ta’addan ke yada farfaganda.
Janar Buratai, wanda Burgediya Janar Timothy Olowomeye ya wakilta a wajen taron horar da Limaman Kiristoci a Sokoto, ya ce sun nemi hadawa da wa’azi da addu’o’i wajen yaki da Boko Haram da ma sauran tashe-tashen hankula.
Ya ce yin amfani da makami kadai da sojoji key i ba zai iya kakkabe ta’addancin Boko Haram ba, amma idan aka samu wata kwakkwarar hanyar da za a yaye masu mummunar akidar da ake cusa masu zai yi tasiri sosai a kan su.
Buratai ya ce, Nijeriya da sauran kasashen duniya da dama sun dade su na fama da rikice-rikicen da ke da nasaba da addini, da tattalin arziki da wadanda ke da dalilai na siyasa.
You must log in to post a comment.