Home Labarai Jami’an Civil Defence Sun Kashe’yan Boko Haram 50 A Jihar Neja

Jami’an Civil Defence Sun Kashe’yan Boko Haram 50 A Jihar Neja

253
0
nscdc oil thieves now use suvs to convey stolen pr nscdc oil thieves now use suvs to convey stolen pr D7098910DDE9BC3CE59D227C183798FC
nscdc oil thieves now use suvs to convey stolen pr nscdc oil thieves now use suvs to convey stolen pr D7098910DDE9BC3CE59D227C183798FC

Rundunar tsaro ta farin kaya ta ce ƴan Boko Haram sun yi wa tawagar jami’anta da ke sintirin ba turakun babban layin wutar lantarkin Shiroro kariya, kwanton ɓauna a jihar Neja.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar Babawale Afolabi ya fitar a yammacin jiya Talata, lamarin ya faru ne a garin Farin Kasa da ke kusa da ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Sanarwar ta ce tawagar na kunshe ne da manyan jami’ai 71 da suka fito daga sassan rundunar daban daban, lokacin da mayaƙan su sama da dari 2 suka kai musu hari, a lokacin

A cewar sanarwar, duk da kwanton ɓaunar da aka yiwa jami’an na Civil Defence, sai da suka samu nasarar kashe sama da mayaƙan masu tada ƙayar baya 50, a musayar mutar da suka yi.

Kakakin rundunar ya kuma tabbatar da cewa jami’an su 7 sun samu raunuka, inda yanzu haka suke samun kulawa a wani asibiti da ke cikin garin Kaduna, sannan wasu 7 kuma sun ɓace inda ake ci gaba da neman su.

An dai tura da tawagar rundunar Civil Defence ne don sanya ido tare da samar da kariya ga turakun layukan wutar lantarki.

sakamakon yawaitar hare-hare da lalatasu da ake yi, wanda ke haifar da katsewar wutar lantarki a faɗin ƙasa.

Leave a Reply