Home Labaru Ilimi JAMB: Hukumar Shirya Jarabawar Gaba Da Sakandare Ta Yi Wa El-Rufai Raddi

JAMB: Hukumar Shirya Jarabawar Gaba Da Sakandare Ta Yi Wa El-Rufai Raddi

226
0

Hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’o’i na kasa JAMB ta mayar wa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i martani kan shawarar da ya bata, ta fasa rage wa ɗaliban arewacin Najeriya makin da ake bukata na jarrabawar.

Hukumar ta ce ba ita ce ke da alhakin ragewa daliban yankin arewacin Najeriya maki ba.

A cewar JAMB, ”Gwamna El-Rufa’i ya yi kuskure da ya yi tunanin cewa ɗaliban arewacin Najeriya na cin wata gajiya da takwarorinsu na kudancin ƙasar basa ci, wannan kuskure ne”

Mai magana da yawun hukumar Fabian Benjaminne ne ya mayar wa gwamnan martanin yayin wata zantawa da manema labarai a ranar Talata.

Ya ce makin da ake bukata ya danganta da kwas ɗin da kowanne ɗalibi ke son yi, da kuma makin da kowacce jami’a ta iyakance.

Leave a Reply