Home Labaru Kanzon-Kurege Ne Labarin Datse Sadarwa A Kaduna — El-Rufai

Kanzon-Kurege Ne Labarin Datse Sadarwa A Kaduna — El-Rufai

221
0

Gwamnatin Kaduna ta karyata rahoton da ake yadawa cewa za ta rufe layukan sadarwa a jihar.

Sanarwar da kakakin Gwamnan Jihar, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Talata ta ce gwamnatin jihar ba ta da shirin rufe layukan sadarwa, kuma ba ta taba tunanin daukar makamancin matakin ba.

Muyiwa ya ce, “Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta tuntubi wata hukuma ta tarayya don neman a dakatar da harkar sadarwa ba kuma ba ta bada umarnin datse hanyoyin sadarwa ba.

“Tana kira ga mazauna jihar da su yi watsi da jita-jitar da ke yawo, saboda labarin karya ne da wasu mutane ke yadawa don goga wa gwamnatin Kaduna kashin kaji.

“Gwamnatin Jihar Kaduna tana fitar da komai a fili game da harkokin tsaro.

Sanarwar ta bayyana cewa, Idan hara aka ga daukar matakin rufe hanyoyin sadarwa ya zama dole to za a sanar a hukumance ta hanyoyin da suka dace.

Leave a Reply