Home Labaru ISWAP Ta Kashe Mutum Uku Da Jikkata Sojoji Takwas A Borno

ISWAP Ta Kashe Mutum Uku Da Jikkata Sojoji Takwas A Borno

288
0

Akalla ‘yan gudun hijira uku ne aka kashe, tare da jikkata
wasu 13 ciki har da sojoji takwas a wasu hare-hare da
kungiyar ISWAP su ka kai karamar hukumar Damboa ta jihar
Borno.

Rahotanni sun ce, lamarin ya faru ne lokacin da ‘yan gudun hijira huɗu da ke zama a sansanin Lowcost a Damboa su ka fita domin neman itacen hura wuta, lokacin da mayaƙan su buɗe musu wuta, inda su ka kashe uku nan take yayin da sauran mutanen kuma su ka tsere da raunuka.

Wata majiya ta ce, tun farko mayakan ISWAP sun jikkata wasu sojoji da fararen hula, yayin wani hari da su ka kai yankin Talala duk a karamar hukumar Damboa.

Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa, sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP da dama a wani hari da su ka kai masu.

Leave a Reply