Mayakan kungiyar ISWAP sun fara raba wa matafiya tarin tsofaffin takardun kudi a manyan hanyoyin yankin da ke kusa da tafkin Chadi.
Rahotanni sun ce, an ga wasu mayakan kusa da kauyen Mariri a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Monguno da ke karamar hukumar Guzamala ta Jihar ta Borno.
Mayakan, sun kasance sanye da kayan yaki na sojojin Nijeriya kuma su na tafiya cikin motocin sulke irin na soji.
Wani ganau ya ce, mayakan sun tsaya a gefen hanyar a karkashin wata bishiya dauke da jakunkuna cike da tsofaffin takardun naira, inda su ka tsaida motar da ya ke ciki daga nan su ka raba wa kowane fasinja naira dubu 100.
Wani wanda ya shaida lamarin, ya ce Mayakan sun gaya masu cewa idan za su iya zuwa banki su sauya kudin zuwa sababbi su yi hakan, tare da yi masu addu’ar cewa Allah ya sa kudin su amfane su.
You must log in to post a comment.