Home Home Sojoji Sun Yi Wa Mayakan Boko Haram Luguden Wuta

Sojoji Sun Yi Wa Mayakan Boko Haram Luguden Wuta

35
0
Nigerian soldiers drive past Government Science secondary school in Kankara, Nigeria, Wednesday, Dec. 16, 2020. Rebels from the Boko Haram extremist group claimed responsibility Tuesday for abducting hundreds of boys from a school in Nigeria's northern Katsina State last week in one of the largest such attacks in years, raising fears of a growing wave of violence in the region. (AP Photo/Sunday Alamba)

Rundunar tsaro ta hadin-gwiwa da ke yaki da mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi, ta kaddamar da wasu munanan hare-haren sama a kan sansanonin mayakan ISWAP domin murkushe su a maboyar su.

Wata sanarwa da rundunar mai dauke da sojoji daga Nijeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi ta fitar, ta ce an kaddamar da hare-haren ne a kan matsugunin ‘yan ta’addar da ke dajin Matari, wanda su ke amfani da shi domin kai hare-hare a garuruwan Maine Soroa da Chetinari da Chetimari Wangou a kasar Nijar.

Sanarwar ta ce an kaddamar da hare-haren ne, bayan an tsinkayi wasu ‘yan ta’adda akalla 50 tsakanin ranakun 27 da 28 ga watan Janairun nan, kuma sojojin Nijar ne su ka kai harin tare da taimakon kuramen jirage masu sarrafa kan su.

Sakamakon wadannan hare-hare, Sanarwar ta ce bayan an lalata sansanonin ‘yan ta’addan, an kuma kama mutane 38 daga cikin su, yayin da wasu da dama su ka gudu.