Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele, ya bayyana a gaban kwamitin kula da harkokin babban bankin kasa da bankuna na Majalisar Wakilai, dangane da sabon tsarin sauya fasalin kudade da kuma daina amfani da tsofaffin takardun kudade.
Majalisar wakilai dai ta tura wa Emefiele sammaci a kan rikita-rikitar da ta biyo bayan sauya fasalin manyan takardun kudade da kuma sauya tsofaffin takardun kudi zuwa sabbi.
Emefiele ya gurfana a gaban Kwamitin wucin gadi da Majalisar ta kafa a karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye na Majalisar Alhassan Ado-Doguwa.
Da ya ke bayani a gaban kwamitin, Godwin Emefiele ya ce bankunan kasuwanci za su cigaba da karbar tsofaffin kudade har bayan karewar wa’adin daina amfani da su zuwa ranar 10 ga Fabrairu na shekara ta 2023.
Godwin Emefiele, ya nuna takaicin sa da yadda wasu ke kawo nakasu ga tsarin sauya fasalin kudin, musammman a bankuna duk da umarnin da CBN ya ba su, ya na mai cewa sun nemi taimakon hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tsaro domin dakile aniyar masu janyo zagon kasa.
You must log in to post a comment.