Home Labaru Inganta Tsaro: Majalisar Wakilan Najeriya Ta Tilasta Wa Hafsoshin Tsaro Bayyana a...

Inganta Tsaro: Majalisar Wakilan Najeriya Ta Tilasta Wa Hafsoshin Tsaro Bayyana a Gabanta Kan Harin Jirgin Ƙasa

147
0

A yau Alhamis ake sa ran shugabannin tsaro na kasa za su bayyana a gaban Majalisar Wakila bayan majalisar ta umarce su da yin hakan a zamanta na ranar Laraba.


Sai dai tun a Larabar shugabannin tsaron suka nemi su gana da shugabancin majalisar ƙarƙashin Mataimakin Kakakin Majalisa Ahmed Idris Wase, amma sai majalisar ta ƙi yarda da hakan, tana mai tilasta musu bayyana a gabanta a yau Alhamis.


Majalisar dai na son hafsohin tsaron su yi mata ƙarin bayani ne game da yadda ‘yan fashi suka kai hari kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum takwas.


Kazalika, tana so ta ji yadda ‘yan bindigar suka kai wani harin kan filin jirgin sama na Kaduna kwana biyu kafin na jirgin ƙasan.


Waɗanda majalisar ke son su bayyana a gabanta sun haɗa da hafsoshin tsaron ƙasa, da sufeton ‘yan sanda na ƙasa, da ministocin da lamarin ya shafi ma’aikatunsu bisa umarnin shugabannin kwamitocin soja da na sufurin jirgin sama da na ‘yan sanda da na sufuri.
Ana sa ran da ƙarfe 3:00 za su bayyana a zauren majalisar.