Home Labarai Harin Jirgin Kasa: Yadda Jami’an Tsaro Suka Gaza Daukar Mataki Duk Da...

Harin Jirgin Kasa: Yadda Jami’an Tsaro Suka Gaza Daukar Mataki Duk Da Bayanan Sirri

62
0

Jami’an tsaro sun gaza dakile harin da ’yan bindiga suka kai kan wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, duk da samun bayanan sirri daga hukumomin tsaro.

Harin da aka kai kan jirgin kasan, mai dauke da fasinjoji sama da 300, shi ne hari mafi muni da aka taba kai wa kan wani jirgin kasa a Najeriya.
Akalla gawarwakin mutum tara aka tsinto daga inda harin ya faru a ranar Talata, yayin da wasu sama da 20 suka samu raunuka sakamakon harbi da kuma turmutsutsu, kana kuma ’yan bindigar suka yi awon gaba da fasinjoji da dama.
Manyan jami’an tsaro sun bayyana wa manema labarai cewa, wasu bayanan sirri sun nuna yadda ’yan bindiga suka jima suna kokarin farmakar jirgin kasa, kuma sun yi gargadi kan daukar mataki amma aka yi burus da su.

Sai dai NRC ta yi watsi da umarnin da hukumomin tsaron suka ba ta kan irin hatsarin da ke tattare da yin hakan.
Manajan Daraktan NRC, Injiniya Fidet Okhiria ya tabbatar da cewa an aike wa da hukumar takarda kan ta daina tashin jirgin kasa da yamma.