Home Home Ta’addanci: Jam’iyyar PDP Ta Kalubalanci Gwamnatin Kaduna Game Da Matsalar Tsaro

Ta’addanci: Jam’iyyar PDP Ta Kalubalanci Gwamnatin Kaduna Game Da Matsalar Tsaro

63
0
Jam’iyyar PDP, ta nuna damuwa a kan harin da ‘yan bindiga su ka a kan jirgin kasa daga Abuja zuwa Abuja, sa’o’i kadan bayan harin da aka a kai a filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna, lamarin da ya yi sanadiyayyar mutuwar ma’aikacin hukumar kula da sararin samaniya ta Nijeriya guda.

PDP ta kuma nuna damuwa a kan yadda a ke yawan kai hari a kan unguwanni da manyan hanyoyi, lamarin da ta ce ba a taba samun irin sa ba a tarihin jihar Kaduna, inda ake kashe mutane baya ga raba wasu da muhallan su kuma babu alamun gwamnatin APC ta dauki matakin kawo karshen lamarin cikin hanzari.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna Felix Hassan Hyat, PDP ta ce ta’addancin da ke waka a jihar Kaduna ba abin da mutane su ka zaba kenan ba, kuma babu wanda ya yi zaton a shekaru bakwai da su ka gabata ‘yan bindiga za su iya mamaye garuwaruwa da manyan hanyoyi da tashoshin jirage, lamarin da ta bayyana a matsayin gazawa bayyananniya.

A karshe ta bukaci al’ummar jihar Kaduna su kwantar da hankulan su, su kuma cigaba da yi ma wadanda su ka rasa rayukan su addu’o’i da ma wadanda ke samun kula a asibitoci.