Home Labaru Korafin Zabe: Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Shugaba Buhari Da Hukumar...

Korafin Zabe: Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Shugaba Buhari Da Hukumar Zabe

476
0

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da bukatar hukumar zabe ta kasa da shugaba Muhammadu Buhari, ta neman kotun ta kori karar da jam’iyyar PDM ta shigar a gaban ta.

Shugaba Buhari da hukumar zabe dai sun bukaci kotun ta kori karar ne bisa dogaro da cewa, jam’iyyar PDM ba ta shigar korafin ta a gaban kotun a kan ka’ida kamar yadda doka ta tanada ba.

Alkalin kotun mai shari’a Mohammed Garba, ya ce jam’iyyar PDM ba ta saba wata ka’ida a karar da ta shigar ba.

Ya ce PDM ta gabatar da duk korafe-korafe a ranar 15 ga watan Afrilu, wanda ya kasance cikin wa’adin da aka tsaida na kammala gabatar da korafi kafin ranar 21 ga watan Afrilu.

Mai shari’a Garba ya kara da cewa, jam’iyyar PDM ta bi tsarin da dokokin zabe su ka tanada, don haka hukumar zabe da shugaba Buhari ba su fahimci yadda lamarin ya ke ba.