Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da wasu kudirori 17 da Majalisar Tarayya zango na 8 ta aika ma shi domin ya sa masu hannu su zama doka.
Ya ce shugaba Buhari ya yanke shawarar ba zai aika wa sabuwar Majalisar wasika a kan kudirorin da ya ki sanya wa hannu ba.
Karanta Labaru Masu Alaka: Albashin Hadiman Buhari, Osinbajo Ya Tsaya
Ita Inang, ya ce zai tuntubi dukkan majalisun dokoki na tarayya domin yi masu bayani a kan dalilin kin amincewar da Shugaba Buhari ya yi na amincewa da kudirorin su zama dokoki.
Ya ce babu wani abu da majalisar yanzu za ta iya yi don tilasta shugaba Buhari ya sa wa kudirorin hannu, domin doka ba ta ba su ikon yin haka ba.
Daga cikin kudirori 17 da shugaba Buhari ya ki amincewa su zama doka akwai Kudirin Jami’ar Adeyemi, da Jami’ar Ilmi ta Jihar Kano, da Jami’ar Alvan Ikoku, da Jami’ar Ilmi ta Zari’a, da kuma Kudirin Dokar Kula da Dabbobi Marasa Lafiya da sauran su.