Home Home INEC Ta Saka Ranar Ƙarasa Zaɓukan Da Ba A Kammala Ba

INEC Ta Saka Ranar Ƙarasa Zaɓukan Da Ba A Kammala Ba

8
0

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta kasa INEC, ta sanya Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za ta kammala zaɓubbukan da ba a ƙarasa ba a Nijeriya.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafin ta na Twitter, ta ce ta yanke shawar ne bayan wata ganawa da ta yi da jami’an hukumar.

Ta ce sai a ranar Asabar 15 ga watan Afrilun ne za a ƙarasa zaɓubbukan gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin da ba a karasa ba sakamakon wasu matsaloli. Hukumar zaben dai ta ayyana zaɓubbukan gwamnonin jihohin Adamawa da Kebbi a matsayin wadanda ba su kammala ba.