Home Labaru Sarkin Muslmi Ya Ce Babu Ranar Da Ba A Kashe Mutane A...

Sarkin Muslmi Ya Ce Babu Ranar Da Ba A Kashe Mutane A Arewacin Najeriya

65
0

Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III ya shawarci  ‘yan Najeriya su hada kai domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasa.

Da yake tsokaci kan matsalar tsaro a Najeriya a taron majalisar hadin kan addinai ta NIREC, Sultan Sa’ad Abubakar ya ce ba lokaci ba ne da mabiya addinai musamman Musulmi da Kirista za su rika zargin juna da yi wa juna barazana ba.

Sarkin Musulmin ya nuna damuwa kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jam’a ke ci gaba da afkuwa, amma kuma Musulmi da Kirista sun bige da nuna wa juna yatsa da yi wa juna barazana.

Mai alfarman  yace dole ne mu daina zargin juna kuma mu hada kai madamar muna son mu yaki makiyan mu…