Home Labarai Ina Cika Alƙawurran Da Na Ɗaukar Wa ‘Yan Najeriya

Ina Cika Alƙawurran Da Na Ɗaukar Wa ‘Yan Najeriya

287
0
President Bola Tinubu commander in chief
President Bola Tinubu commander in chief

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce gwamnatin sa tana cika alƙawuran da ta yi wa jama’ar ƙasa.

Tinubu wanda ya taya ƴan Najeriya murnar cika shekara 25 kan mulkin dimokuraɗiyya babu katsewa,

ya kuma nemi haɗin kan al’umma domin samar da kyakkyawar ƙasa da za ta zamo abin alfahari ga ƴan baya.

Ya yi gargaɗi a kan jefa dimokuraɗiyya cikin mawuyacin hali yana mai cewa dole ne a ci gaba da haɗa kai wajen gina ƙasa,

da kuma jaddadawa a koda yaushe, cewa ba a da wata ƙasa da ta fi Najeriya.

shugaba Tinubu ya nemi haɗin kan ƴan majalisar da ma sauran jama’ar ƙasa wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatin sa da kuma bunƙasa Najeriya.

Shugaban Najeriyar ya kuma nemi goyon bayan majalisar wajen kammala aiki a kan kasafin kuɗin da ya gabatar mata,

wanda ya ce zai taimaka wajen aiwatar da tsare-tsaren da gwamnati ke da su, masu muhimmanci ga jama’ar ƙasa.

Leave a Reply