jam’iyyar RHDP mai mulki ta bayyana shugaban kasar a matsayin dan takarar da za ta gabatar a babban zaben
Kakakin kawancen kawancen jam’iyyun da ke mulkin na kasar Gilbert Koné Kafana ne ya bayana haka, a wani mataki na yi wa Shugaba Ouattara tayin tazarce,
duk da yake shugaban bai fito karara ya bayyana manufarsa ba. Gilbert Kafana ya ce Alassane Ouattara ne dan takarar jam’iyyar
da ke mulki,
kana za mu bukace shi ya amince da wannan kuduri idan lokaci ya yi. Mai shekaru 82 a duniya Shugaba Ouattara na kan karagar mulki
ne tun a shekarar 2011,
bayan wa’adi na biyu shugaban ya sake kundin tsarin mulki a wani mataki na ci gaba da kasancewa kan madafan iko.