Home Labarai Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyukan Layin Jirgin Kasa Na Abuja

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyukan Layin Jirgin Kasa Na Abuja

69
0
311fc9e8d370a3c8
311fc9e8d370a3c8

Tinubu ya kaddamar da layin dogo na Abuja,wanda ke nuna wani gagarumin ci gaba a harkar sufurin ,

Bikin ya samu halartar manyan jami’ain gwamnati da suka hada da mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa, alkalin alkalan , da sauran manyan baki.

A jawabin sa, shugaba Tinubu ya bayyana matukar alfahari da godiya bisa ganin yadda aka samu nasarar gudanar da wannan aiki,

inda ya bayyana hakan a matsayin shaida na sadaukar da kai da hangen nesa na gwamnatin sa.

Shugaban ya tunatar da cewa, layin dogo na Abuja wanda aka fara aikin tun shekarar 2018 na gwamnatin baya da ya gada,

ya fuskanci koma baya sakamakon annobar COVID-19 da kuma yin watsi da tasgaro da aikin ya rinka fuskanta.

Shugaban ya bayyana amincewar sa da muhimmiyar rawar da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya taka,

yace ministan yayi abin a yaba masa kuma yana alfahari dashi ganin yanda nasarar aikin ya wuce tsammani.

Leave a Reply