Hukumar Kula da Ilmin Mata ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta ce akalla ana bukatar karin malamai mata kusan dubu 58 da 121, wadanda za a yi amfani da su wajen koyar da yara dalibai mata a Arewacin Nijeriya.
UNICEF ta ce yin haka zai zama matakin farko na kokarin cike gibin da ke tsakanin yawan dalibai maza masu samun ilmi da kuma dalibai mata masu samun ilmi a Arewacin Nijeriya.
Hukumar dai ta yi wannan bincike ne a cikin shekara ta 2018 a jihohi takwas na Arewacin Nijeriya.
An gudanar da binciken ne domin kokarin inganta yawan kananan yara mata a makarantu da ke Arewacin Nijeriya.Jihohin da aka yi binciken a cikin su kuwa sun hada da Bauchi da Gombe da Katsina da Kebbi da Neja da Sokoto da Taraba da kuma Zamfara.