Home Labaru Maslaha: Da Alamun Onnoghen Zai Yi Murabus Da Kan Sa

Maslaha: Da Alamun Onnoghen Zai Yi Murabus Da Kan Sa

295
0

Alamu na nuna cewa, dambarwar da ke tsakanin tsohon shugaban Alkalan Nijeriya mai sharia Walter Onnoghen da gwamnatin tarayya ya zo karshe, domin yanzu haka ana sa ran Onnoghen zai yi murabus da kashin kan sa.

Wata majiya ta ce majalisar sharia ta koli ta aika wa shugaba Buhari rahoton binciken da ta gudanar, inda ta nemi a ba Onnoghen damar yin ritaya cikin mutunci, biyo bayan karar sa da gwamnati ta shigar a kan wasu makudan kudade da aka gano ya mallaka ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma, Onnoghen ya kulle kariyar da ya ke ba kan sa a wannan shari’a, tun bayan kawo shaida guda daya, wanda hakan alamu ne na saduda kamar yadda masana shari’a su ka bayyana.

Majiyar ta ce idan har Onnoghen ya yi murabus, lamarin zai zame masa tamkar gobarar titi, domin zai iya karbar naira biliyan 2 da rabi a matsayin kudin sallama.

Haka kuma, gwamnati za ta gina ma shi gida a Abuja, sannan a kashe ma shi naira biliyan daya wajen kawata gidan, yayin da za a ba shi kudin ajiye aiki da yawan su ya kai ninki uku na albashin sa kamar yadda doka ta tanada.