Home Labaru Tattalin Arziki: Shugaba Buhari Zai Bar Nijeriya Zuwa Kasar Jordan

Tattalin Arziki: Shugaba Buhari Zai Bar Nijeriya Zuwa Kasar Jordan

416
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai je kasar Jordan a wani mataki na amsa gayyatar Sarki Abdullah II bin Al-Hussein domin halartar taron kungiyar tattalin arziki ta duniya da za a gudanar a Dead Sea da ke Jordan.

Buhari zai gabatar da jawabi yayin bude taron, tare da Sarki Abdullahi II bin Al-Hussein da babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres.

Daga nan kuma za su hadu da sauran shugabannin tattalin arziki na duniya a wani taron da zai gudana a cibiyar taro ta Sarki Hussein Bin Talal.

Shugaban Buhari, zai kuma yi ganawa mai muhimmanci da wasu shugabannin dunniya bayan taron, daga nan zai wuce kasar Dubai domin halartar taron zuba jari na tara da ake yi duk shekara a ranakun 8 da10 ga watan Afrilu. Buhari zai zamo bako na musamman a wajen taron, sannan zai yi jawabi mai taken ‘Share Fagen Zuba Jari na kasa-da kasa kai tsaye’. 

Leave a Reply