Home Home Ilimi: Manya Da Ƙananan Ma’aikatan Jami’o’i Za Su Bi Sahun ASUU Zuwa...

Ilimi: Manya Da Ƙananan Ma’aikatan Jami’o’i Za Su Bi Sahun ASUU Zuwa Yajin Aiki

152
0
Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i da gamayyar Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya NASU, sun ba Gwamnatin Tarayya wa’adin a cika masu alƙawarin su nan da ranar 27 Ga watan Maris ko kuma su kulle jami’o’in a rasa mai zuwa aiki.

A Cikin wata wasiƙa da kungiyoyin su ka aika wa Ministan Ƙwadago Chris Ngige, sun zargi Gwamnatin tarayya da ƙin cika masu alƙawarin da ta ɗauka cikin Oktoba na shekara ta 2020, da wani da ta ɗauka duk a rubuce a cikin watan Fabrairu na shekara ta 2021.

Kungiyoyin dai sun aika wa ministan wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren kungiyar NASU Peter Adeyemi da kuma Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, inda su ka bada wa’adin ko dai gwamnati ta magance matsalolin su ko kuma ta fuskanci yajin aiki.

Sun ce sun yi mamakin ganin cewa, duk sharuddan da su ka gindaya wa gwamnain tarayya, amma har yau ba ta yi wani abu ko da guda ɗaya ƙwaƙƙwara ba.