Home Home Tsaro: An Sa Dokar Hana Walwala A Kananan Hukumomin Jema’a Da Kaura

Tsaro: An Sa Dokar Hana Walwala A Kananan Hukumomin Jema’a Da Kaura

89
0
Gwamnatin jihar Kaduna, ta sa dokar hana walwala ta tsawon sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura, sakamakon tashin hankali da barke a yankunan.

Gwamnatin jihar Kaduna, ta sa dokar hana walwala ta tsawon sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura, sakamakon tashin hankali da barke a yankunan.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

Samuel Aruwan, ya ce an sa dokar ne domin jami’an tsaro su iya shawo kan tashin hankalin da ya ɓarke, kafin ya yaɗu zuwa wasu sassan yankunan da ke karkashin kananan hukumomin.

Ya ce da zarar an samu natsuwa da kwanciyar hankali gwamnati za ta sanar da inda aka dosa. Kwamishinan ya yi kira ga mutanen jihar Kaduna su kwantar da hankalin su, domin gwamnati da jami’an tsaro su na aiki tukuru wajen kawo karshen matsalolin rashin tsaro a fadin jihar.