Home Labaru Tuna Baya: Dalilin Da Ya Sa Na Sauka Daga Kujerar Mulki A...

Tuna Baya: Dalilin Da Ya Sa Na Sauka Daga Kujerar Mulki A Shekara Ta 2015 – Jonathan

301
0
Goodluck Jonathan, Tsohon Sugaban Kasa
Goodluck Jonathan, Tsohon Sugaban Kasa

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce kyautata zaton makomar dimokradiyya a nahiyyar Afirka ta sa ya hakura ya mika wa shugaba Muhammadu Buhari mulki a shekara ta 2015.

Jonathan, ya bayyana haka ne, yayin gabatar da jawabi a wajen taron kara wa juna sani a kan al’amurran da su ka shafi harkokin zabe da ya gudana a Abuja.

Ta bakin mai magana da yawun sa Nze Akachukwu, Jonathan ya ce ya sadaukar da kudirin sa na ci-gaba da mulkin Nijeriya domin tabbatar da kyakkyawar makomar dimokradiyya a nahiyyar Afirka.

Jonathan, ya kuma yaba wa abokanan arziki da kungiyoyi masu fafutikar kare hakkin dan Adam da su ka dauki nauyin shirya taro, domin tunawa da akidun marigayi Oronto Douglas da ya mutu a shekara ta 2015.

Leave a Reply