Home Labaru Bayyana Kadara: Mai Shari’a Walter Onnoghen Ya Daukaka Kara

Bayyana Kadara: Mai Shari’a Walter Onnoghen Ya Daukaka Kara

285
0

Tsohon shugaban alkalan Nijeriya mai shari’a Walter Onnoghen, ya daukaka kara a kan hukuncin da kotun da’ar ma’aikata ta yanke ma shi bisa laifin kin bayyana biyar daga cikin asusun bankunan sa da ke dauke da tarin kudaden ketare.

Onnoghen ya gabatar da korafe-korafe guda 16 a gaban kotun daukaka kara da ke a Abuja, jim kadan bayan kotun da’ar ma’aikatan ta yanke ma shi hukunci.

Daya daga cikin korafe-korafen da ya gabatar, Onnoghen ya kafe cewa bai taba amsa laifin ya aikata laifuffukan da kotun ta zarge shi da su ba.

Takardar daukaka karar ta kara da cewa, mai daukaka karar bai amsa laifin kin bayyana dukiyar sa daga shekara ta 2005 a matsayin sa na mai shari’a a kotun koli ba.

Ta ce mai daukaka karar kawai ya bayyana cewa, bai bayyana ba ne a shekara ta 2009 kamar yadda aka bukata, saboda ya manta, kuma nan da nan ya bayyana bayan ya gano hakan.’

Walter Onnoghen ya kara da cewa, kotun da’ar ma’aikatan ta yi kuskure a tsarin shari’a, a kan korar korafin da ya shigar na kalubalantar ikon ta na yi ma shi shari’a, wanda hakan ya keta haddin shari’a.