Home Labaru Ikirari: Kungiyar ISWAP Ta Dauki Alhakin Kashe Sojojin Nijeriya Biyu

Ikirari: Kungiyar ISWAP Ta Dauki Alhakin Kashe Sojojin Nijeriya Biyu

920
0

Kungiyar IS reshen yammacin Afirka ISWAP, ta fitar da wani bidiyo da ya nuna yadda mayakan ta su ka kashe wasu mutane biyu da ta ce dakarun sojin Nijeriya ne.

Haka kuma, Kungiyar ta ce ta kama sojojin ne a farkon watan Satumba, yayin da mayakan ta su ka kai hari wani barikin soji a jihar Borno.

Kawo yanzu dai, rundunar sojin Nijeriya ba ta tabbatar da ikirarin na Boko Haram da ke cewa mutanen da ta kashe sojojin ta ne ba.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Mayun da ya gabata, kungiyar ta fitar da wani bidiyo da ya nuna yadda ta hallaka mutune tara da ta ce dakarun sojin Nijeriya ne.