Home Labaru Wata Sabuwa: An Kama Wata Mata Da Ta Saci Jariri Saboda Ba...

Wata Sabuwa: An Kama Wata Mata Da Ta Saci Jariri Saboda Ba Ta Haifi Da Namiji Ba

680
0

Jami’an ‘yan sanda a jihar Ekiti, sun kama wata mata mai suna Mercy Momoh bisae zargin ta da satar jariri dan watanni biyu a Ado-Ekiti.

An dai kama matar ne a gidan ta da ke yankin Odo-Aremu da ke babban birnin jihar, kuma sace jinjirin ne daga mahaifiyar sa Funmilayo Sunday a sakatariyar jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Caleb Ikechukwu ya tabbatar da kama mai laifin, inda ya ce yanzu haka ana kan gudanar da bincike.Da ta ke yi wa jami’an ‘yan zandan bayani, mai laifin ta ce ta saci jinjirin ne saboda tsananin bukatar mallakar da namiji, ta na mai cewa, sakamakon rashin haihuwar da namiji, mijin ta ya sake auren wata matar sannan ya kore ta daga gidan shi.

Leave a Reply