Home Labaru Sufuri: Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna Ya Dauki Fasinjoji milliyan 1...

Sufuri: Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna Ya Dauki Fasinjoji milliyan 1 Da Dubu Dari 5 A Kwana 1000

280
0

Shugaban hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya Fidet Okhiria, ya ce a cikin kwanaki dubu 1, jirgin kasa ya yi sufurin akalla fasinjoji milliyan 1 da dubu dari 5 daga Abuja zuwa Kaduna.
Shugaban hukumar, ya bayann a hakne a lokacin da yake magana a taron murnar wannan nasara, ya ce jirgin ya yi aiki na tsawon kwanaki dubu 1 ba tare da hadari ba, ko kuma wata matsala ba, kuma bai bar aiki kona kwana daya.
Ya ce duk da haka mutane na kokawa cewar hukumar ba ta gudanar d aiki yadda ya kamata, amma komai a hankali yake tafiya, inda ya bayar da tabbacin cewa za su kara yawan adadin jiragen zuwa karshen shekaran nan.
Fidet, ya kara da cewar akan maganar siyar da tikiti ta yanar gizo kuwa, su na ci gaba da aiki akai, amma wajibi ne su bi komai a hankali.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne dai ya kaddamar da aikin jirgin a ranar 26 ga watan Yulin 2016, wanda shi ne jirgin safarar mutane na farkon da wasu injiniyoyin kamfanin kasar China suka gina ta hanyar biyan kashi 75 na kudi da kuma kashi 25 daga Nijeriya.

Leave a Reply