Home Labaru Idan Na Zama Shugaban Ƙasa Sai Na Fi Buhari Aiki Tuƙuru –...

Idan Na Zama Shugaban Ƙasa Sai Na Fi Buhari Aiki Tuƙuru – Okorocha

43
0

Sanata Rochas Okorocha, ya ce ya na so ya yi takarar kujerar shugaban kasa a shekara ta 2023, domin ya fitar da ‘yan Nijeriya daga ƙuncin talauci, ya na mai shan alwashin cewa zai zarce Shugaba Buhari wajen yin aiki tuƙuru.

Okorocha ya ce, tabbas Shugaba Buhari ya yi wa Nijeriya da ‘yan Nijeriya ayyuka da dama, amma idan ya zama shugaban ƙasa ayyukan da zai yi sai sun ninka na shugaba Buhari nesa ba kusa ba.

Sanatan ya bayyana haka ne, yayin da ya ke gabatar da kan sa a matsayin wanda zai fito takarar shugaban kasa a zaɓen shekara ta 2023.

Tun a makon da ya gabata ne, Sanata Okorocha ya sanar da ‘yan Majalisar Dattawa cewa zai fito takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, sai dai Hukumar EFCC ta maka shi kotu a ranar da ya ke ƙaddamar da kan sa.